Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wasu jami’ai a gwamnatin Taliban sun bayyana cewa suna gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen kai hari, yayin da ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta sanar da Alhakin kai harin a masallacin da mabiyar mazhabar shi’a da sunna suke halarta
A baya bayanan dai kasar Afghanistan na fuskantar hare-hare a masallatan juma’a da kungiyar Ta’adda ta Daesh ke kaiwa tun bayan da kungiyar Taliban ta karbi jan ragamar shugabancin kasar
Wata majiyar Asibitin a garin ta nuna cewa akalla mutane 3 sun mutu yayain da wasu 15 kuma suka jikkata halin wasu daga cikinsu ya munana sosai,
342/